abdul adamu sani wudil
Abubuwan Da Ake yiwa Tsarki:
Anayin tsarkine daga dukkan abin daya fito ta daya daga mafita guda biyu kota duka biyun, amma banda hutu wato (tusa). Ana yiwa ♠ Fitsari. ♠ Bayangida. ♠ Maniyyi. ♠ Maziyyi. ♠ Jinin al'ada. ♠ Tsarki. kawai dai idan mutum yanada alwala sai yayi tusa to alwalar kawai zai sake basai ya dauki buta yayi tsarkiba. Hukuncin Tsarki: Tsarki wajibine, saboda haka dukkan wanda dayan wadancan abubuwa da makamantansu suka sameshi to dole ya tabbata ya gabatar dayin tsarki.