Fa idodin aure ko dalilin yinsa
*yan uwana matasa yana da kyau musancewa komeye a addinin nan namu na muslinci da aka umarce muyi zakaga yana da faidoji sosai musali alwala babbar faidar ta mutsarkaka daga najasa harma da zunubi,mukoyi tsafta
to hakama aure yana da fa idoji kamar haka
*dan mucika umarnin Allah swt ,acikin Alqur ani me tsarki cikin suratul nisa'i waje farko farko
yace ku auri daga abun da ya dadada gareku na daga mata,wato ka/ki auri wanda ya kwantamiki a rai
ashekenan yin aure cika umarnin Allah da manzansane s.a.w
*2 samun ziriya tagari ,da kare mutum daga fitowa tahanyar zina
3*aure na kange dan adam daga biyan buqatar sa ta sha awa a haram ,da sahuran su
*4 aure na samar da al umma tagari wadan da annabi s.a.w zai yi alfahari dasu
*5 kasancewar sa ibadane dole kakoyi haquri da juriya nutsuwa da qara hankali sakamakon kasan nauyin ciyar wa kula da magai dawainiyar ilminta dana yayanta yadawo kanka ,
shawara ta garemu matasa aure dai ibadace ,kowanna ibada tana da matakai ladubai hukunce hukunce sanin su da yin aiki dasune ke iya sa a sami ma aurata nagari masu samar da al umma tagari
ABDUL ADAMU SANI wudil
07033031695
Allah kashiryamu