Abdul haruna sani
Kaicon mu yan uwa
*Aliyu bin Abi Dalib Allah ya kara masa yarda yace Manzon Allah s.a.w yace "Idan har al'ummata ta rika aikata abubuwa guda goma sha biyar to bala'i ya sauka kenan cikin wannan al'ummar sai akace wadanne abubuwane wadannan ya manzon Allah? Sai yace
Idan dukiyar baitil mali ta zama tana zagayawa a tsakanin wasu mutane su kadai banda wadansu to su saurari zuwan bala'i a kasa
Idan zakka ta zama kamar haraji mai tsanani a wajen masu dukiya {mawadatansu basu fitar da zakkar dukiyarsu su bawa mabukata} to ku saurari bala'i a kasa
Idan amana ta zama ganima ga wadanda aka baiwa ita a saurari bala'i a kasa
Idan kaga mutum yana girmama abokinsa yana wulakanta mahaifinsa saurari zuwan bala'i a kasa
Idan kaga mutum yana girmama matarsa yana wulakanta mahaifiyarsa a saurari zuwan bala'i a kasa
Kuma idan shugaban jama'a ya zama shine wulakantaccensu{bashi da mutunci} a saurarai zuwan bala'i a kasa
Kuma idan kaga ana girmama mutum saboda tsoron sharrinsa a saurari zuwan bala'i a kasa
Kuma idan kaji sautuka suna daukaka {hayani da rikici cikin jam'a} a saurari bala'i a kasa
Idan kaga yawaitar shan giya iri daban-daban da amayar da ita kamar ba haramun ba ce a saurari bala' a kasa
Ko ka ga ana ado da alhariri a saurari zuwan bala'i a kasa
Ko kuma yawaitar kayan kade kade da goge-goge a saurari zuwan bala'i a kasa
Ko kuma samun cudanya tsakanin maza da mata {kamar gurin party da sauransu} a saurari zuwan bala'i a kasa
Kuma idan kaga ana koyon karatun addini ba domin neman yardar Allah ba sai domin neman duniya ko domin a burge wadansu ko don ayi alfahari dashi a dushe hasken wasu babu kyakkyawar niyya a ciki {kamar yanda yake faruwa a yanzu} a saurari bala'i a cikin kasa
Idan mafi fasikancin mutane ya zama shine shugabansu {wannan sanannen abu ne a cikin mu} to a saurari zuwan bala'i a kasa
Idan ka ga wannan al'ummar ta karshe tana zagin wacce ta gabace ta {a kowane fage kamar yanda wasu ke zagin sahabban manzon Allah s.a.w bacin sun gaba ce su} a saurari zuwan bala'i a kasa
To iadn irin wadannan fitinu da bala'o'i su ka rika faruwa to mutane su saurari zuwan wata jar iska ko kuma nutsarwa ko shafewa daga Allah
Tirmizi ne ya ruwaito
by Abdul Adamu sani wudil |