Abdul adamu sani wudil
CUTAR QANJAMAU (HIV/AIDS) NA CIGABA DA YADUWA KAMAR WUTAR GONA A QAUYUKA.
Wannan cuta mai matuqar hatsari me karya garkuwan jikin dan adam wato qan jamau har yau nacigaba da yaduwa acikin al'umma tamkar wutar gona .
Abun tausayin tana matuqar yaduwa a qauyika .
Tafi kuma hallaka mutanen qauyuka akan na burdi sakamakon mutanen qauye sukan kamu da cutar har tai qarfi ajikin su batare da sunga likitaba ,dakuma rashin kudade ko duhunkai,
DALILIN DA YASA QAN JAMAU TAFI YADUWA A QAUYUKA A YAU.
* sakamako yawaita mutanen qauye dake zuwa burni cin rani ko tashi tsahon wasu watanni,da yawansu sukan yi bariki da matan banza wadansu kuma daga matan banzannan sunsan suna dauke da qanjamau, amma dan mugunta ko dan karsu kashewa kansu kasuwa basa amfani da hanyar kariya idan mutum ya buqaci hakan,
a irin wadannan yawace yawacen ne maza suke kwaso wadannan ciwon ya zo kuma gida wato qauyen su ya zubawa matansa ,inbashi da aure kuma yazubawa yan matan gari da zawarawa mazunata suma suyi ta yadata ga fasiqai yan uwan su.WANNAN ITACE HANYAR DA QANJAMAU TAFI YADUWA A QAUYUKA.
*hanya tabiyu tahanyar yin amfani da kayan kaifi kamar aska qaho da shauran su. Itama wannan hanyace dake tai makawa wajen yaduwar qan jamau a qauye .SAIKAGA SAMA MUTUM GOMA A MAJALISTA ANTARU, GA WANZAMI GUDA DAYA ,YANA BINSU DAYA BAYAN DAYA YANAIMUSU ASKI KO GYARAN FUSKA ,DA ASKA DAYA KUMA sannan ba kuma tsaftace kayan askin sukeba kamar yadda yadace dan suna sauri suyiwa wani ,wani da aska daya zai shiga kasuwar qauye yaitaiwa mutane aski ,sai dai yawasata bayan yagamaiwa wani kafin yasami wani, KADANNE DAGA CIKIN WANZAMAI MASU KULA DA KAYAN ASKINSU. HAKAMA YA TAIMAKA WAJEN YADUWAR QANJAMAU A QAUYE.,
**HANYOYIN KARIYA***
# YANA DA KYAU WANZAMAI SUKARBI TSARIN ZAMANI NAYIN ASKI DA REZA GUDA GA KOWANNA MUTUM DAYA ,DA MAKANAR HANU, KODA A QAUYUKA SUKE.
# YANA DA KYAU KAFIN AYIMA ASKI KATABBATA WANZAMI YA QONE ASKARSA YAKUMA GOGE TAS.IDAN KANA QAUYENE
# ZAIFI KYAU KASAI REZAR NAIRA GOMA MATARKA TA ASKEMA KANKA HAKAN SHIYAFI KWANCIYAR HANKALI.IDAN BA WANZAMAI MASU KULA DA SANA AR.
# SHIMA QAHO INYAZAMA DOLE SAI ANYI TO KA TABBATA AN WANKESHI CIKI DA WAJE DA RUWAN CHEMIKAL TAS SANNAN AN FIQE WATO ANKANKARE BAKINSA INDA AKASAWA WANI .
# YANA DA KYAU ANA YIN KWAJIN QANJAMAU KAFIN AYI AURE A QAUYIKA GA MATASA MASU ZUWA CIN RANI KO KULE KULEN MATAN BANZA.
# LALLAI MASU ZUWA CINRANI SUJI TSORAN ALLAH SUDENA ZINACE ZINACE ,IDAN AKWAI DAMA SUNA TAFIYA DA MATANSU NEMAN KUDIN HAKAN ZAI BASU KARIYA DA GA ZINA.
# IDAN MASIFAR TAKAI MASIFAR DA BAZA A IYA HAQURA DA ZINABA TO LALLAI AYI AMFANI DA KWANDOM WATO KWARORON ROBA.
# YANA DA KYAU ANA DAUREWA ANA ZIYARTAR MALAMAN LAFIYA DAN BADA SHAWARWARI AKAN HARKAR LAFIYA KO IN ANGA ALAMUN RASHIN LAFIYA.
#LALLAI MALAMAI SUCIGABA DA FADAKAR DA MUTANEN KARKARA AKAN SHARRIN DA ZINA KE JANYOWA DA HANYOYIN DA ZA A GUJETA.
# YANA DA KYAU GWAMNATI DA QUNGIYOYIN SAKAI SUNA QARA DAGEWA WAJEN WAYAR DAKAI A QAUYUKA AKAN ILLOLIN WANNAN CUTAR DA YADDA AKE KAMUWA DA ITA DA YADDA ZA A KIYAYE.
# YANA DA KYAU GWAMNATI DA KUNGIYOYIN SAKAI SUNA SAMAR DA HANYOYIN YIN GWAJIN QANJAMA KODA A BOYENE GA MUTANEN QAUYE DAN GANO MASU DAUKE DA CUTAR DABASU MAGUNGUNA DA SHAWARWARI DA WURI.
# YANA DAKYAU MALAMAI DAMASU UNGUWANNI KO SARAUTA SUMA SUBADA HADINKAI WAJEN KULA DA LAFIYAR AL UMMARSU TAHANYOYI DADAMA.
*Matan aure salihai katan gaggu na mutuwa dayawa sakamakon kanjamau a qauyuka.
*dattijai na kwasar ciwannan a askar wanzamai.
*samari yan cirani dayawansu na dauke da cutar qan jamau ajikin su amma ba asaniba.
ALLAH YAKARE MU DUKKAN MU NABIRNI DANA KARKARA.AMEEN
by Abdul Adamu sani wudil |