DALILAI GUDA 12 DAYA SA JAM' IYYAR APC RASHIN NASARA A ZABEN 2023 A KANO STATE (NIGERIA).
(1). Rashin shigar da Qarin girma ga malaman makaranta (promotion) musammanma malaman primary da shauran kananan ma aikatan Local Government dake kano state, dayawan malaman primary suna bin gwamnati bashin promotion wasu tun kusan shekaru 10 ba promotion babu wani dukkan nau'in kudi dasunnan inganta walwalar su, Kusan dukkan malamin primary da Yamutu da ga shekaru 8 zuwa yau ,muna iya Cewa tabbas yamutu da baqincikin rashin promotion a ransa. Dukda haka gwamnati tayi wani yunquri nayin promotion ga malaman primary tun kusan na shekaru 10, malamai sun kwallafa rai akan za ayi musu promotion amma sai da aka zo jajiberan zabe gwamnati taki yimusu, sai ma tabisu da tabbatar da qarin shekaru 5 na ritaya, tabbas wannan ya harzuqa malaman primary da bata musu rai dayawa sun kuma dauki alwashin daukar fansa, Hakika dayawan malaman primary sun bada gudummawa wajen kada gwamnatin APC
(2). A bangare daya ga matsalar da yan fansho suke fuskanta, na rashin biyan su akan lokaci da yanke yanken wani kaso daga cikin fanshan su batare da wani dalili ba, su ba ma ta batun garatuti suke ba a a bukatar su adena yankar musu fanshan su.
(3). Halin Matsin rayuwa da al' umma suke fuskanta na qaqa nakayi a sakamakon qarancin wadataccen takardun kudi a hanun mutane dakuma irin asarar da wasu kananan yan kasuwa sukayi dukka a sakamakon sauya fasalin kudi da jam iyar APC tayi shima wannan ya qara janyowa jam iyar baqinjini a gun su al'umma.
(4). Laifin wasu ya shafi wasu hakika jam iyyar APC Ta Tara yantakara kala kala da wadanda suka batawa mutane basu kyautata ba, sai Sai wadanda basu iya kalamai ba kullun kalaman su na jawo cecekuce akwai yan ba ruwanka akwai kuma mutanen Kirkir wadanda mutane na kaunar su dan sun kwatanta musu adalci masu kima hakan yasa har gobe suke musu zaton Alkairi, irin wadannan bayin Allah Sam bai kamata su fadi zabe ba, Amma laifin wasu ya jamusu, Aban gare daya kuma wannan matsalar ta qara haifar da wata matsalar Inda mutane idon su ya rufe sukai ta zabar har wadanda basu da inganci na wata jam iyar dandai sugar sun kayar da Jam iyyar APC sun rama ko Dan huce haushi. Dukdai awannan maganar yana daga abunda yakara tasiri wajen kayar da jam iyyar APC rashin tsai da yan Takara masu qwari da kima a idon jama' a awasu dai dai kun kujerun takara.
(5). Suma yan kasuwa damasu kananan sana o'i sun taimaka wajen kayar da jam iyyar APC,
(6). Dalibai na makarantun Gaba da secondary sun bada tasu gudun mawar wajen kayar da jam iyyar APC ,yana daga batu mafi girma da suka fi batu akai dashi rashin tallafin karatu tun a lokutan baya, gakuma batu akan tsarin da gwamnati tace zata debe su aikin empowerment na KAHUCEE tsahon lokaci shuru kakeji, hakanan dalibai yan bodin suma sun bada tasu gudummawar wajen kifar da gwamnatin APC.
(7). Sakin wani video da yadinga zagayawa acikin Al'umna dake dauke da wasu jagororin jam iyyar APC cikin wani qaton rumbun ajiya da ke shaqare da kayan abunci ,Wanda ake zaton tallafin korona bairos ne tun a shekarun baya a ka bawa gwamnatin ta rabawa al' umma, suka bada wani suka ajiye wani sai yanzu da zabe yazo suka son suyi amfani dashi ,hakika hakan yakarawa jam iyyar APC baqin jini a idon al'umma harda masu goyan bayan jam iyyar abun bai musu dadi ba, hakan hatta wasu daga cikin malaman addini suma sunyi batu akai
(
. Kodai rashin ingantattun masu bada shawara tagari kokuma in anbada shawarar ba a dauka
Dole asami daya a wadannan musali ,rana a tsaka aka tayar da sikirinin na malaman primary da sunan za ayimusu promotion haka akai ta jujjuya maganar tsahon watanni 4 sai da zabe yazama shaura kwana 4 malamai suka sami yaqinin da tabbaci na ba za ayi musuba wannan ya haifar da zazzafan martani a kafafen sadarwa irin su facebook, WhatsApp har ma wadanda ba malamai ba suka San halin da ake ciki.
Musali na biyu shine akwai yan Takara masu kwaliti wadanda zasu iya kawo akwatinan su, da kujerun da ake nema amma tun akan rabon mukamin shugabancin jam'iya akafara bata musu rai da maidasu yan kallon.
(9). Yin amfani da kayan abunci kamar taliya da atamfofi memakon kudi, dayawan iyayen mu mata a karkara zaka iya yaudarar su da taliya da atamfa amma banda matasa da yan birni, mutane sunfi son kabasu kudi Susa a aljihu koda zasu zabeka amma ba kabasu taliya ko atamfa a hanu kowa yana ganin su da ruku ruku dan kowa ita yasan tamaye.
(10). Faduwar wasu sanatoci da repa repai na jam'iyyar APC shima yasa wasun su janye hannun su,
(11). Gajiya Da Al'ummar jahar kano tayi da mulkin APC
(12). Gwamnatin APC gwamnatice wacce take cike da zargi kama daga na sayar da filaye da rage Ragen wasu filaye mallakin jahar kano da shauran zarge zarge da akeyiwa gwamnatin shima ya taimaka sosai wajen kada wannan gwamnati
Allah katemaki jahar kano a kowannan ma taki dama kasar mu Baki daya, Dafatan zababbiyar Gwamnati zata hada kai da kowanna ma aikaci batare da nuns bambancin jam iyya ba.
Abdu Adamu Sani Wudil
07033031695
UNDER MAINTENANCE