Abdul adamu sani wudil
SHIN WAI MENENE DADIN DUNIYA?
ace yau duk fadin duniyar nan ba ka da na biyu a tarin dukiya, ko me?
Gidaje da mutum ya tara manya manya?
ko makudai da ke cikin banki tari tari?
kyawawan mata da mutum ya ajiye, a narka-narkan gidaje ?
Koko tarin ’ya’ya da mutum ya samu, su ne alamun mutum ya samu abin jin dadin duniya?
Shin rashin matsaloli na rayuwa, komai ya yi wa mutum daidai, kana ci, kana sha, kana shaqatawa wannan shi ne jin dadin rayuwar?
Shin tufatuwa da tufa da ta fi kowace tsada da burgewa, shi ne jin dadin rayuwar ko me?
Dan yau abin hawa na gani da fada ya zama abin hawa a gare ka, ka shiga wancan dankareriyar mota, ka hau jirgi ko kuma kai ne da jiragen sama ko na ruwa, naka na kanka shi ne jin dadin rayuwar?
Koko mulki dama ,kasa akashe kasa a kama ,kasa a saki shine dadin duniya?
YAN UWA DUKKAN SU WADANNAN BA SUNE DADIN DUNIYABA .
domin inkudine ne dadin duniya ina dan qaruna ,?
Nawane masu kudi suke cikin tashin hankali AMMA KUDIN YAQI YIMUSU MAGANI MATSALAR SU?
nawane tarin dukiyar su yajefasu halaka?.
*in kace kyawawan mata sune dadin duniya TO MATANAWA NE KYAWAWA WADANDA SUKA DAUWA MA ?
duk kyan matarka watarana dakanka zakaga wacce tafita kyau amma kai lokacin ka ya wuce kana so kuma KAKAGA KYAUN MACE BASUNE DADIN DUNIYA BA KE .
bawani da baya rayuwa da matarsa irin yadda kakeyi da taka kyakkyawa matar.
*in kace manyan gidaje sune dadin duniya to ai bawani mahaukacin katafaren gida da bazai zama kangoba ko kushewa ko me dadewa
nawane wadanda basu da gidan kan su AMMA SUNA RAYUWA ME KYAU ?.
*inkace mulki da dama ,to nawane masu mulki basa cikin kwanciyar hankali kuma mulkin bai magani ba?
Nawane mulkin su da shugabancin su yazama kurku a takura da nadama atare da su ?
*inkace tarin abun hawa ne jin dadin duniya TO watarana kai za a dauko abun hawa mafi wulaqanci,
nawane wadanda basuda da abun hawaba amma suna rayuwa me dadi?
ASHE KENAN DUKKAN SU BASUNE DADIN DUNIYABA ,ILLA DAI KAWAI , WANI DAN DADINE QALILAN NA DUNIYA DA ALLAH SWT YAKE BAWA WASU DAGA CIKIN BAYINSA DAN KAWAI YAJARRABE SU .
TO INHAKANE MEYE DADIN DUNIYA?
dadin duniya yan uwa shine RAYUWAR ADDINI
WATO
*RAGE BURI
babu wani abu mafi quntatawa dan adam a rayuwa irin buri, INKANA DA BURI GUDA GOMA KAYI 9 TO HANKALINKA BAI KWANCIYA BAJIN DADI ,me kudi yafi marar kudi buri ,me mulki yafi marar mulki buri IYA YAWAN BURINKA IYA YAWAN WAHALARKA.
Kagama primary burinka ,kaje secondary ,inkaje burinka kaga kayi candy ,dakayi candy burinka kasami jam kasami addm a jami ah,daganan mastarin digiri ,daganan dacta,dagananan sokake kazama farfesa ,daganan SOKAKE KAZAMA A FROFESA MA KAINE KAFI KOWA ,HAKAMA DAN KASUWA,KO MEKUDI,KO ME MULKI ,BURIN SU SUZAMA,SUNFI KOWA,
* TAWAKALLI.
Ba abunda yafi tawakalli dadi da dauwamar da kwanciyar hankali ga dan adam da dauwamar da dadi in kasamu kasan ALLAHNE IN KARASA KASAN DAGA ALLAHNE ,IN MASIFA TASAME KA KASAN DAGA ALLAH NE IN KAI KOMAI MA SAI KAGA MUTUM YASAMI DADIN DUNIYA KENAN.
*HAQURI :babu abunda yafi haquri da dadi da kwanciyar hankali irin haquri, inka rasa sai kayi haquri in anma badai daiba sai yahaqura batare da yasa damuwa ba a ransa
IDAN ALLAH swt YABAKA HAQURI ,TAWAKKALI,WADATAR ZUCI,DA,DA RASHIN BURI TO ALLAH YAGAMA BAKA DADIN DUNIYA DA NUTSUWARTA ,KODA BAKA DA KOMAI DAGA DUKIYA ,KUDI,MATA,SARAUTA ,YAYA DA SHAURANSU.
ashe kenan dan uwa Dan Allah swt yaiyoka talaka to karka dauka Allah swt bai sonka ,koko bai son kaji dadiba.
Hakanan dan Allah swt yauyoka mekudi ,ko mai yaya,ko mulki ,ko yabaka mata kyawawa KADA HAKAN YASA KADAUKA ALLAH KAI YABAWA DADIN DUNIYA KADAI ,
kawai Allah swt yabaka wani dan bangare ne nadadin duniy qalilan ne.
* WADATAR ZUCI
* TAWAKALI
* DOGARO GA ALLAH
* SAMUN MACE TA GARI
dukkan su suntabbata a hadisan annabin mu s.a.w ingantattu.
ALLAH YABAMU DADIN DUNIYA ME ALBARKA


