Ring ring

DANYIN TAMBAYA KO NEMAN SHAWARA ZABI GIDA DAYA KA SHIGA A NAN KASA
HOMEZAMAN AUREJAVA|HTML CODE

ADDINISOYAYYALAFIYA
Joint our WhatsApp Group

nan
12026-02-04
*Post reply · Invite friends · From end
Abdul Adamu sani wudil HAIHUWA BAIWAR ALLAH.

*ALAMOMIN DA IN ME CIKI TAGANSU TO AKWAI ALAMUN MATSALA SAI TA JE ASIBITI.

1* matsanancin ciwon ciki da riqewar mara kamar na ciwan al'ada

2* mace taji luuu kamar zata suma

3* dan zubar jini ko bleeding

WADANNAN ALAMOMINE DAKE NUNA WATAQILA MACE TASAMI MATSALA WATO ECTOPIC PREGNANCY. wato dancikinta baya zaune a inda yakamata ya zauna wato uterus.

Sannan zubar da jini da riqewar mara matsananci a satukanta nafarkon samun ciki zuwa sati na 12 ko 13 wato first trimester hakan shima alamace ta mace zata iyayin bari.

*4 matsanancin tashin zuciya da amai .

*5 ganin ruwa yana bin qafarki ,bakuma fitsariba

*6 matsanancin ciwonkai,matsanancin ciwon ciki ,matsalar gani da kumburin jiki a lokacin sa tuttukan kusa da haihuwa da ma na haihuwa wato third trimester, wannan zai iya zama alamar cutar PREACLAMPSIA.

*6 alamomin mura matsananci kamar FLU SYMPTOM .

Wadannan nasaman dukkan su alamomine dasuke nuna a iya samun matsala. Amma ba lallaine ba. ANASO INKINJI IRINWADANNAN KODA BA RANAR AWUN CIKIN KiNE BA TO KIJE KIGA LIKITA.

GAKUMA WASU ALAMOMI IN ANGAN SU NANUNA MACE NACIKIN HATSARI SOSAI .SAI AYI GAGGAWAR ZUWA ASIBITI.

*1 wato mace taga alamomin haihuwa a satukan ta kamar na 20 zuwa sati na 37 wato( PRETERM LABOUR )na cikinta .tabbas akwai matsala gareta dakuma abuncikinta

2* ganin alamar ansami ciki saikuma a ga alamar bari kamar zubar da jini da gudaguda,riqewar mararki kamar na ciwon al ada..

3* budewar gaba irin na kusa da haihuwa ,a lokacin da ba na haihuwa ba .

*4 da shauran su

Wadannan na nuna alamar matsala babba gareki maza kije asibiti.

QANANAN MATSALOLIN MACE ME CIKI DA YADDA ZA A RAGE MATSALAR.

*1, GIRMAN NONO .hakan ba matsala.

*2 yaiyon nono kadan ko madara madara kamar colostrum. Hakan ba matsala amma kizama me tsafta ,wanka sa rigar mama me soson tare ruwan nonon.

*4 GAJIYA. Sabo da qarancin ion ko kuma yarcikinki na zuqar sana daran qara girma .dan haka kina shan magungunan da aka baki a gun awun ciki akwi na qara ion,

kina dan tattaki a tsakar gida kamar go and come sau goma koda ahankali.

4*tashin zuciya da dan amai .yafi tsanani da safe ko in baki ci abunci ba , KINA CIN DANGIN ZANGANNIYA NA ABUNCI KAMAR GERO ,SHINKAFA KO IRIN SU TOES .SANNAN KUMA AMAI DA TASHIN ZUCIYA BA MATSALA NEBA GA MAICIKI DAZARAR KINYI WATA 4 ZAKI DENA YI. yakan iya zama matsa in yazama matsananci.

5* YAWAITAR FITSARI AKAI AKAI: sakamakon abun cikinki yana kada uterus itakuma uterus sai ta matsi bladdarki saikina jin fitsari nandanan MUSAMMAN A SATUKAN KI NA FARKO WATO SATIN FARKO ZUWA NA 13 DA KUMA WATANKI NA HAIHUWA WATO first and second trimester of pregnancy. KADA KINA SA MATSATSTUN KAYA.
SANNAN KADA KINA BARIN MARARKI DA FUTSARI.

*6 CIWON KAI: saboda gajiya ko hayaniya ko canjin sana darai.
Abun da zakiyi shine ,KINA DAN WATSA RUWA ME DAN SANYI AKANKI, KINA SAMUN GU ME NUTSUWA KI KWANTA KIHUTA BA HAYANIYA, kifadawa likitanki ko kya iyashan tylenol dan ciwon kai.

*7 ganin dan jini da kumburi a baki ko hanci kojin danqo danqo abaki.
KINA YAWAITA BRUSH DA WANKE FUSKARKI.

*8 ATINI KO KASHI ME TAURI .
kiyawaita shan ruwa sosai kamar glass 6 ko 8 na ruwa dakuma glas 1 ko 2 na ruwan wasu abun shan wato fluid

*9 JIRI KO DAUKA ,KAMAR ZAKI SUMA .
YADDA ZAKIYI SHINE IN KIN DADE A TSAYE KAFIN KIFARA Jin JIRIN SAI KI NA DAN MOTSAWA KIYI TAFIYA KADAN KO KITASHI KI ZAUNA KAMAR SAU 2.

*9 WUYAR BACCI.
kina shan ruwa dayawa,kina shan madara me dan dumi in bata saki ciwon ciki. ,wanka da ruwan dimi kafin ki yi bacci,kina kwanci da fulo 3 daya a wuyanki ciki, da guiwarki .

*10 tasowar zuciya da zafinta:
Kizama kina cin abunci a hankali daya bayan daya .
Yazamana kina cin abunci lokaci lokaci kadan kadan kuma,shan abu mai dan dimi,kada ki kwanta da zarar kinci abunci ,kada kihada abunci mai maiqo dame zaqi kici a lokaci daya. Kitambayi likitanki ko zaki iya amfani da magani kamar mylanta,riopan ko gaviscon.

11* dan rauni ko zafi a tubura.
Kibar tsaiwa a tsaye lokaci mai tsayi kina dan wanka da ruwan dimi mafi qaranci lokaci a rana .

12* kumburin qafa.
Kibar tsaiwa a tsaye lokaci mai tsaho.kina motsa qafarki lokaci zuwa lokaci, kibar sa takalma ko wando mai dame qafa ,kina motsa jiki.

13*riqewar qafa ko sagewa.
Kina cin abunci me sanadarin calcium kamar madara ,chees,kina motsa qafarki inkin dade a zaune.,kina motsa jikinki.

14*.YAYYON HANCI NA MURA.
kina danna ruwan dimi a fuskarki,
kibar fesa body sprey sai kintambayi likitanki.
,kina shan ruwa da yawa ,in zaki kwanta kina sa fulo a wuyanki dan hana toshewar maqogoro,kina wanka da ruwan dimi inkina da wannan matsalar.

ATAQAICE YAR UWA DAN KULA DALAFIYARKI DATA JARIRINKI SAIKINBI WANNAN SHAWARWARIN.

*ZUWA AWU BISA QA IDA.
*AMFANI DA MAGUNGUNAN DA DAKTA YABAYAR.
*CIN ABUNCI MAI GINA JIKI DA QARA LAFIYA.
*MOTSA JIKI
*SAMUN HUTU,NUTSUWA ,BACCI
*KULA DA JIKI BIN SHWARWARIN DAKTA
*TSAFTA.

DOLE MAIGIDA KATAIMAKI UWAR GIDA DA

*KAYAN QARA LAFIYA KODA MARASA TSADANE KAMAR ZOGALA.
*Bata hutu


07033031695
2015-09-20 05:28 · Reply · (0)
Yahaya adamu adamu * Abdul Adamu sani wudil Masha Allah
2016-07-28 04:19 · Reply · (0)

Online: Guests: 1

2963622
HOMESpeedCounter.net - Free web counter
Share Button
© 2012 TO 2022 www.arewa2.wap.sh created by Abdul Adamu Sani Wudil
1
SAHEN LABARAN HAUSA
Aminiya
hausa radiyo
Almi'izan
hausa leadership
voa hausa
trt hausa
rfi hausa
dw hausa
bbchausa
cri hausa
A A
AIKO SAKOSMSKIRA© 2020 arewa2.wap.sh
call 07033031695

l
sss