XtGem Forum catalog

DANYIN TAMBAYA KO NEMAN SHAWARA ZABI GIDA DAYA KA SHIGA A NAN KASA
HOMEZAMAN AUREJAVA|HTML CODE

ADDINISOYAYYALAFIYA
Joint our WhatsApp Group

nan
12026-01-10
*Post reply · Invite friends · From end
Abdul Adamu sani wudil CUTAR TARIN TIBI (tuberclusis).

Wannan wani azababban ciwone da kowa yasan shi ko yake jin labarin sa.

Shidai tarin tibi ciwone dake iya shafar gurare daban daban ajikin dan adam kamar hanji, kashi da gabobi ,fatar mutum ,bargo hunhu da shauran tsokar jiki.

Idan tarin tibi ba ayimasa magani ba yakan iya haddasa wadancan illolin yayiwa mutum fatafata yamaidashi abun tausayi kamar kwarangwal.

ALAMOMIN CIWAN SUNHADA. DA

* MATSANANCIN TARI SAMA DA SATI 3 ME HADE DA MAGINA KO BABU MAJINA.

* TARI DA JINI

* ZAZZABI
* CIWAN QIRJI
* NINFASHI SAMA SAMA
* SIRANCEWA DA RASA NAUYI
.


AKAN IYA SAMUN WASU ALAMOMIN KAMAR.

* CIWO DA KUMBURIN GABOBI
*RASHIN QARFI SOSAI A QAFAFU
* RIQEWAR WUYA
* GUMIN JIKI
* RIKICEWA WATO DIMUWA
* RASHIN HAIHUWA IDAN YASHAFI GABOBIN HAIHUWA.

yakan iya shafar ko ina ajiki shi yasa ma yake da alamomi da illoli da yawa ,sannaan illarsa da alamomin idan yai qarfi sukan banbanta daga wani me cutar zuwa wani mecutar yadan ganta da inda ciwan yaje yakama SAIDAI YAFI KAMA HUNHU SHIYASA AKAFI GANIN WADANCAN ALAMOMIN NAFARKO.



* MEKE KAWO TARIN TIBI?*

wannan ciwan yanafaruwane idan mutum ya sami yawu ko majina ,atishawa,tari ko makamantan su daga me ciwan to shima zai iya dauka matuqar akwai kwayar cutar tarin tibi aciki wato kwayar bacteria wacce ake kira MYCO BACTERIUM TUBERCULOSIS. To mutum zai iya kamuwa koda ta hankicine ko tsumma matuqar ansami misayar sanadaran baki ko hanci to za a iya dauka.

Tarin tibi ciwone dayai barna sosai a afurka kasashe masu tasowa yakashe mutane dayawa idan yazo gida sai yakashe kamar mutum 5 ko sama da haka. Ko ya nakasta wasu kamar matsalar hunhu koda anwarke

kumaa ciwone me saurin yaduwa daga wani zuwa wani


amma ayau ana warkewa matuqar anje asibiti kuma anbi dokar likita.

Shan maganin sa na qa ida da dokoki danhaka atabbata ansha qarqashin kulawar likita.


HANYOYIN KARI DAGA TARIN TIBI.

* BADA ILMI GA ALUMMA AKAN YADDA ZASU KAUCEWA KAMUWA DA CUTAR TAHAN YAR KARE KAI.

* ME CUTAR YAGUJI SHIGA AL UMMA ,YAKUMA DINGA YIN AMFANI DA HANKICI WAJEN KARE BAKINSA YAYIN TARI ,ATISHAWA DA SAURANSU.

* adinga tsaftace hanu abunci ,kayan wasan yara.

* ayi gaggawar zuwa asibiti dazarar tari ya haura sati 2 bayan kuma ansha maganin tari amma ba sauqi DAN YIN GWAJIN TARIN TIBI.

* yawaita tsaftar kayan abunci agida a kiyayesu daga kudaje kyankyasai da shauran su.

ALLAH YABADA LAFIYA.
2017-04-25 13:47 · Reply · (0)

Online: Guests: 1

2962156
HOMESpeedCounter.net - Free web counter
Share Button
© 2012 TO 2022 www.arewa2.wap.sh created by Abdul Adamu Sani Wudil
1
SAHEN LABARAN HAUSA
Aminiya
hausa radiyo
Almi'izan
hausa leadership
voa hausa
trt hausa
rfi hausa
dw hausa
bbchausa
cri hausa
A A
AIKO SAKOSMSKIRA© 2020 arewa2.wap.sh
call 07033031695

l
sss