Hadisi na 1
An karbo daga sarkin muminai, baban Hafs, Umar bin khaddabi yace naji Manzon Allah (SAW) yana cewa ''Lallai kadai, ayyuka suna tare da niyyoyinsu, kuma lallai kowane mutum yana samun sakamakon abin da ya yi niyya (a zuciyarsa). Wanda duk hijirarsa ta kasance saboda Allah da Manzon sa, wanda kuma hijirarsa ta kasance saboda duniya da zai samu, ko don wata mace da zai aure ta, wannan sakamakon hijirar sa na nan kan abin da ya yi hijira zuwa gare shi.'' Shugabannin masu hadisai ne suka rawaito shi. Su ne Muhammad dan Isma'ila dan Ibrahim dan Mugirata dan Bardizbah Al-Bukhari Al-Ju'ufiy. Da Abul Husaini Muslimu dan Hajjaju dan dan Muslimu Alqushairiy Annaisaburiy. Acikin ingantattun littattafan su.


