Abdul adamu sani wudil
ABUBUWA 6 DA DAN ADAM KE MATUQAR BUQATARSU A RAYUWARSA.
*1 TSARO
*2 LAFIYA
*3 ABUNCI
*4 SUTTURA
*5 MUHALLI.
*6 ILMI
DAN ADAM YANA DA WASU BUQATU NA DOLE A RAYUWAR SA A KOWANNA HALI YAKE NA RAYUWAR SA ,
da yarasa wani daga cikin su to ya tagaiyara sosai ,GASU KAMAR HAKA.
*1 TSARO.
shine qashin bayan cigaban kowacce al umma a dauniya ,
duk wata al umma data ci gaba ta samu ingantaccen tsarone dashine arziki ke yaduwa ,asake ayi kasuwanci asami riba sosai ,datsaro ne ake samu aje makaranta ayi karatu cikin kwanciyar hankali .
Da tsarone ake samu a qulla soyayya har ayi aure a hayayyafa danhaka tsaro na sahun gaba acikin buqatun dan adam
DUKKAN AL UMMAR DA TA RASA TSARO TO ZAKASAME TA ABAR TAUSAYI SAKAMAKON CIBAYANTA DA LALACEWARTA.
2* LAFIYA.
Lafiya itace buqata ta dan adam tabiyu bayan tsaro domin komai sai da lafiya ake samu ayi IDAN BA LAFIYA KOMAI ZAI TSAYA CAK.
YANA DAGA BABBAR MATSALAR QASATA NAJERIYA TA BABBAREWAR HARKAR LAFIYA .
yara qanana na mutuwa a sakamakon qananan cututtukan da za a iya magance su dawuri amma tarin matsaloli na harkar lafiya yasa ana ji ana gani dubunnan yara namutuwa.
Hakama mata masu haihuwa da shauran su YANA DAGA BABBAN SAKACI DA GWAMNATIN NAJERIYA TAKEYI GAME DA LAFIYA SHINE RASHIN BAWA MUTANE ILMI AKAN LAFIYA WATO (HEALTH EDUCATION)
sai dai qungiyoyi daga waje (n g o) suzo sune zakaji suna ta shirye shirye akafafen yada labarai akan yadda za a magance cututtuka da shauran su.sukan shiga bunni da qauye su ilmantar da al umma amma ita gwamnatin qasa qoqarin ta kadanne.,HARYAU CUTUTTUKAN DASUKE QANANA WADANDA KAMATA TAI ACE ANMANTA DASU AMMA A YAU 75 % sune suke kashe mutane .
*3 ABUNCI
shine babbar buqatar dan adam bayan lafiya da abuncine ake samun kuzarin yin kowanna aiki tundaga kan tunani ko aikin qarfi dole sai anci abunci ake iyawa.
Dukkan al ummar data rasa abunci to tana cikin bala i babba ,
qarancin abunci na haifar da mace mace da cututtuka kala kala
. Qananan yara sunfi shiga bala i yayin rashin abunci .
Rashin abunci kan sa dan adam aikata kowanna irin ta addanci a duniya.
*4 SUTTURA .
suttura na abu na hudu da dan adam ke buqata da zarar hankalin ya kwanta yasami tsaro an duba lafiyarsa yaci abunci to abun da zai fara nema sutturar da zai rufe tsaraicin sa..
*6 MAHALLI
yana daga cikin buqatun dan adam na dole ,dan da mahalline ake fakewa daga rana ,ruwa iska ko sanyi da da tsare dukiya da surrun zaman takewa .dole ne a kowanna hali dan adam yake yana buqata mafaka(muhalli).
*6 ILMI.
ilmi shine gishirin zaman duniya da ilmine ake samar da tsaro ,dashine ake samar da magani dagano cututtuka dashine ake samar da sutturu da muhalli ASHE KENAN DAN ADAM YANA MATUQAR BUQATAR ILMI . DOMIN IN BAKA BASHI ILMI BA TO BAZAI ZAUNA LAFIYA BA (BA tsaro), in ba ilmi zai ta aikata abubuwan da zasu kawo cututtuka da shauran su ataqaice dai ilmi shine qashin bayan cigaban dan adam.
WADANNAN SUNE MANYAN ABUBUWA DAYAKAMATA SHUWA GABANNIN MU A KOWANNA MATAKI SUNA SAMARMANA SHI. KUMA YADDA YAKAMATA
YAZAMA WAJIBI AKAN KOWANNA SHUGABA YASAMARWA DA TALAKAWAN SU ABURNINE KO AQAUYENE IYA IYAWARSA IN KO YAQI KO YA TAUYE WATA DAMA DAGA CIKIN DAMAR DA YAKE DA ITA TO ALLAH BA ZAI BARSHI BA ZAI KAMA SHI AKAN WANNAN DAMAR KOMAI QANQANTAR TA
ranar gobe qiyama kowanna me mulki a kowanna mataki za azo dashi adaudaure da sarqa BABU ABUN DA ZAI KUNCE SHI SAI ADALCIN SA. KOMAI QANQANTAR MULKIN DA AKABAKA
..
ME YAKE SAWA SHUWA GABANNIN MU GAZAWA WAJEN SAMAR MANA DA WADANNAN ABUBUWA?
*1 RASHIN ZABAR SHUGABAN DA YADACE.
mafiya yawan shuwa gabannin mu basu cancantaba
kafin mutum yazama shugaba yakamata yacika wasu sharadai .
*2 RASHIN SAMUN MATAIMAKA NAKIRKI.
wasu shuwagabannin namu nakirkine kuma suna da kyakkyawar manufa amma a sakamakon rashin samun ma aikata na kirki wadan da zasu wakilce shi amata kai na kowanna bangare. Daya sukan ha inci shugaban su.
*3 RASHIN HUKUNTA SHUGA BAN DA AKA KAMA DA BADAQALA.
kowannan shugaba in yai barnarsa kusan kowanna dan qasa burni da qauye sunsan barnar da yai amma ba za a hukuntashiba sai ma abashi kariya ta musamman DA HAKANE KOWA YAKE TSULA TSIYAR SA IN YA HAU MULKI YASAN SURUTUNE KAWAI ATA KARDA.
*4 KARAN CIN ILMI DA RASHIN WAYEWAR TALAKAN QASA.
sun san shugaba ba nagari bane amma sune zasu je su zabe shi dan dan wani abu qalilan su sai da yan cin su.
*5 KWAIKWAYAR MULKIN TURAWA.
Da yawan shuwa gabannin mu a mulkin su sudai burin su su kwaikwayi turawa da sungano tsari a qasar turai yadace da qasar mu ko bai dace ba a a sudai kawai ace sune suka kawo abu ko a mulkin sune aka fara kaza.
*6 RASHIN KISHIN QASA.
daya wan shuwa gabannin da akeyi basu da kishin qasa hakan tasa kazawar su ta fito fili .BA YADDA ZA AI KAHADA SHUGABAN CIN ME KISHI DA WANDA BA ME KISHIBA .kishi ne kesa mutum jajurcewa a kan aikin sa.
ALLAH KATE MAKI QASAR MU NAJERIYA KA ALBARKACE TA DA SHUWA GABANNI NAGARI.
09073717289



